Nijar ta karbi ganyen shayin madagaska don maganin cutar korona

Rahotanni sun ce Nijar ta karɓi ganyen tazargade da za a iya shayi da shi wanda shugaban Madagascar Andry Rajoelina ya ce yana maganin cutar korona.

Kamfanin dillacin labaran AFP ya ambato jami'i a ma'aikatar lafiya Souley Zaberou na tabbatar da cewa sun karɓi ganyen kyauta daga Madagascar.

Madagascar ta yi iƙirarin cewa ganyen tazargade ya warkar da masu cutar korona cikin kwana 10, kuma tana fatan rabawa sauran kasashen Afirka domin maganin cutar.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce gwaji bai tabbatar da ganyen yana maganin korona ba, kuma babu wani binciken masana da ya tabbatar da yana magani.

Nijar na da mutum 755 da suka kamu da korona zuwa yanzu, yayin da cutar ta kashe mutum 37 ciki har da ministan ƙwadago Mohamed Ben Omar, kamar yadda alƙalumma na baya bayanan da suka nuna, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito mana

Comments